Mace mutum

posted by | Leave a comment

Wannan su ne matakai da suke kai wa ga saba wa Allah da keta huruminsa, da cin amanar farji da rashin kiyaye hakkinsa, sai Imam (a.s) ya yi umarni da yanke asasin farko shi ne kallon sha'awa da kawar da kai daga kallon juna.

Sai kuma ya gindaya wasu hanyoyi masu muhimmanci da zasu iya zama hanyar ladabtar da farji ya shiga taitayinsa, domin kawar da shi daga saba wa Allah da kutsawa cikin haram, yana mai cewa: "da kuma ba shi kariya da yunwa da kishirwa idan ya yi nufi, da yawaita ambaton mutuwa, da kuma gargadi ga kanka saboda Allah, da tsoratar da ita da shi, kariya da taimako suna ga Allah ne, kuma babu dubara ko karfi sai da shi".

A cikin littafin Nahajul-balaga: Hikima ta 27- ya zo cewa: An tambaye shi game da imani sai ya ce yana kan ginshikai hudu ne: akan juriya, da yakini, da adalci, da jihadi: A- Hakuri yana kan rassa hudu: akan shauki, da tsoro, da zuhudu, da taka-tsantsan: wanda ya so aljanna zai fidiye (ya fita) daga shaawaice-shaawaice, wanda ya ji tsoron wuta zai nisanci haram, wanda ya yi gudun duniya zai ga saukin musibu, wanda ya yi sauraron mutuwa zai gaggauta zuwa aikata alherai.

Sannnan a cikin littafin sakon hakkoki na Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma kuma hakkin farjinka shi ne ka kare shi daga zina, ka kiyaye shi daga abin da bai halatta ba, ka taimaka a kansa da rufe idanuwa, domin shi ne mafi taimakon abu, da kuma ba shi kariya da yunwa da kishirwa idan ya yi nufi, da yawaita ambaton mutuwa, da kuma gargadi ga kanka saboda Allah, da tsoratar da ita da shi, kariya da taimako suna ga Allah ne, kuma babu dubara ko karfi sai da shi".

Amma idan da babu irin wannan doka, sai aka kama shi da sunan shari'a aka yi masa ukuba, to ya zama zalunci, domin ba yadda Allah zai halicci mutum, sannan sai ya hana shi hanyar mafita kan halittar sha'awa da ya yi masa.

Ibn Abbas yana cewa: "Mutu'a rahama ce da Allah ya tausaya wa wannan al'umma da ita, ba domin Umar ya hana ta ba, da babu wanda zai bukaci yin zina sai tababbe".

Sai ya ginda ya masa wadannan hanyoyi masu kima da daraja da maganin taurin kan sha'awa wacce ba ta jin maganar hankali ba ta bin umarninsa, kuma ba ta jin gargadinsa.

Wato wanda ya hadu da wata mace farkon abin da yake faruwa tsakaninsu shi ne kallon juna, sai kuma su yi wa juna magana, sai su sanya inda zasu hadu, sai kuma su hadu kan sabon Allah.

Jabir dan Abdullah yana cewa: "Mun yi auren mutu'a lokacin manzon Allah (s.a.w) da lokacin Abubakar, da wani bangare na lokacin Umar, sai Umar ya hana" (Bidayatul Mujtahid, na Hambalawa: 2 / 63).

Mash'huriyar maganar Imam Ali (a.s) ta shahara cikin musulmi cewa: "Ba don Umar ya hana auren mutu'a ba, da babu wanda zai yi zina sai ya tabe".

Da yawa zamu ga wani rashin imani da babu kamarsa, idan mun bincika sai mu samu ba dan halala ba ne ya yi shi.

Da sharrin zina ya tsaya kan haka ne kawai da ya isa sharri, domin yana hana kamalar dan Adam, hada da kazanta da take yawaita da yada cututtuka marasa iyaka a cikin al'umma, ga kuma hana ruwan sama da arziki da zai iya mamaye al'umma sakamakon zina.

Leave a Reply

Free chat raw sex